Asalin hoton, Family

A makon nan ne wasu mutane da ake zargin ƴan bindiga suka hallaka shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria MACBAN, reshen karamar hukumar Takum na jihar Taraba, Alhaji Ibrahim Saidu.

Rahotanni sun bayyana cewa ƴanbindigar sun buɗe masa wuta lokacin da suka afka gidansa da ke anguwar Rogo, a yammacin ranar Lahadi.

Ƴanbindigar sun tsere jim kaɗan bayan hallaka shi, lamarin da ya jefa yankin cikin fargaba da ɗimuwa.

A tattaunawarsa da BBC, shugaban Miyetti Allah na jihar Taraba, Alhaji Ya'u Ibrahim Barewa, ya ce sun kaɗu matuka da jin labarin kashe Alhaji Ibrahim Saidu.

'Yadda aka kashe shi'

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 zuwa 8 na yammacin ranar Lahadi, inda wasu mutane kan babur suka buɗe masa wuta a kofar gidansa, lokacin da ya yi ƙoƙarin tashi ya buɗe kofa, a cewar shugaban na Miyetti Allah na jihar Taraba.

"Shi kaɗai lamarin ya shafa babu wani daga cikin iyalansa da abin ya rutsa da su," in ji Alhaji Ya'u Ibrahim.

Bayan faruwar lamarin sun sanar da hukumomin tsaro domin ganin an ɗauki mataki na cafke waɗanda suka aikata kisan.

"A halin yanzu dai jami'an tsaro na ci gaba da bincike domin kama masu laifin.

End of Wanda aka fi karantawa

Ya ƙara da cewa tuni aka naɗa wani kwamiti na musamman don gudanar da bincike.

Wane hali ake ciki a yanzu?

Shugaban na Miyetti Allah na jihar Taraba, Alhaji Ya'u Ibrahim ya ce ana can ana cikin juyayi da zaman makoki a karamar hukumar Takum kan rasuwar Alhaji Ibrahim Sa'idu.

Ya kwatanta marigayin a matsayin mutum mai son zaman lafiya wanda yake zaune lafiya tsakanin manoma da makiyaya.

Yana kuma aiki kafaɗa da kafaɗa da jami'an tsaro wajen ganin an samu zaman lafiya a yankin.

"Ana cikin ɗimuwa kan kisan da aka yi wa Alhaji Ibrahim saboda mutum ne na gari," in ji Ya'u Ibrahim.

Ya ƙara da cewa hukumomin tsaro a karamar hukumar ta Takum na can suna aiki tukuru don ganin an kamo waɗanda suka aikata ɗanyen aikin cikin gaggawa.

End of content

'Shugaba jajirtacce'

Shugaban na Miyetti Allah ya ce an yi babban rashi da kisan Ibrahim Sa'idu saboda yadda yake tafiyar da abubuwansa tsakani da Allah.

"Miyetti Allah a Taraba da kuma ƙananan hukumomin jihar sun yi rashi na adalin shugaba, wanda aka san shi da son zaman lafiya.

"Babu abin da za mu yi iya da abin da Allah ya aika. Mun yi rashin Yallaɓoi," in ji Ya'u Ibrahim.

A cewarsa, suna son gwamnatin jihar Taraba ta matsa ƙaimi wajen ganin an kama waɗana suka kashe shugaban na MACBAN.

"Ranar da aka kashe shugaban MACBAN na Takum, a wannan daren da misalin karfe 2 zuwa 3, an kuma kashe wani Arɗo Shirye a Rafin Kada a karamar hukumar Wukari. Ka ga a nan dole ne jami'an tsaro su tashi haikan don ganin zaƙulo masu aikata wannan ta'asa," in ji Alhaji Ya'u Ibrahim.

Wane ne Ibrahim Sa'idu?

Ibrahim Saidu dai ya kasance makiyayi kuma sananne wanda ya taɓa shugabantar matasa a karkashin ƙungiyar Miyetti Allah na Takum II.

Yana kuma zama a yankin Kashimbilla.

Har ila yau, ya kuma taɓa jagorantar ƙungiyar ƴan banga na Kashimbilla.

Sai mukamin rikon ƙwarya na shugaban Miyetti Allah na karamar hukuamr Takum na tsawon watanni shida.

"Bayan haka, aka soke shi tare da yin zaɓe, inda ya samu nasara na zama shugaban Miyetti Allah na Takum ranar 10 ga Disambar 2015," in ji Ya'u Ibrahim.

Ya rasu ya bar mata uku da ƴaƴa 16.

Mutum ne da ya kasance yana noma da kuma kiwo, wadda ita ce sana'ar da aka fi saninsa da ita.

Abin da ƴansandan suka ce

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rundunar ƴansanda a jihar Taraba ta tabbatar da kashe shugaban Miyetti Allah na jihar, reshe karamar hukumar Takum, Alhaji Ibrahim Saidu, bayan buɗe masa wuta da ake zargin wasu ƴanbindiga sun yi masa a kofar gidansa.

Wata sanarwa da kakakin ƴansanda jihar, ASP Victor Mshelizah ya fitar, ta ce tuni ta kaddamar da bincike don gano mutanen da suka aikata ta'asar domin gurfanar da su gana shari'a.

Sanarwar ta ce kwamishinan ƴansandan jihar, CP Edwin Ogbehagha ya ba da umarnin ɗaukar duk matakan da suka dace domin gano abin da ya janyo aka kashe shugaban na Miyetti Allah.

Ƴansandan sun kuma ce suna aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin ƙarfafa tsaro a yankunan da abin ya shafa da kuma tabbatar da cewa ba a ƙarya doka da oda ba.

‎Don haka ne rundunar ta buƙaci al'ummar yankin da lamarin ya faru, musamman iyalan mamacin da kuma ƴan uwansa da su kwantar da hankali da kuma guje wa ɗaukar matakin da zai jawo bazuwar rikici ko kuma harin ramuwa.

Karanta karin labarai

Kashe ƙwarƙwatar ido

Karshen Kashe ƙwarƙwatar ido

Babban Labari

Wane ne shugaban Miyetti Allah da aka kashe a Taraba?

Me ke janyo kwaɗayin dare bayan cin abinci?

Labarai na musamman

Labaran da suka fi shahara